Rasuwar Shugaban Kasar Austriya | Siyasa | DW | 07.07.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Rasuwar Shugaban Kasar Austriya

Shugaban kasar Austriya Thomas Klestil ya rasu yana da shekaru 71 da haifuwa

Shugaban kasar Austriya, marigayi Thomas Klestil

Shugaban kasar Austriya, marigayi Thomas Klestil

Kwanaki biyu kafin kammala wa’adin shugabancinsa karo na biyu ga kasar Austriya Shugaban kasa Thomas Klestil ya rasu bayan da ya sha fama da radadin ciwon zuciya. Da farkon fari dai an shirya zai danka ragamar shugabancin ga magajinsa mai jiran gado a jibi alhamis idan Allah Ya kai mu, amma sai ga shi kaddara ta rutsa da shi. Tun daga shekarar 1996 ne tsofon shugaban na kasar Austriya yake fama da cita a huhunsa, inda daga baya-bayan nan muryarsa ta dusashe saboda wahalar numfashi, kamar yadda aka lura lokacin da yake jawabin kwantarwa da al'umar kasar hankalinsu dangane da yakin da Amurka ta gabatar kan kasar Iraki. Kimanin shekaru 12 marigayi Klestil yayi yana shugabancin kasar Austriya ya kuma taka muhimmiyar rawa wajen dawo wa da kasar martabarta da ta zube a idanun duniya sakamakon gardandamin da aka sha famar yi dangane da tarihin rayuwar magabacinsa akan wannan mukami Kurt Waldheim. Bayan da jam’iyyar Austrian People’s Party, ÖVP a takaice, ta nada shi domin takarar neman mukamin shugaban kasar ta Austriya, ya sami kafar lashe zabe har sau biyu. An dai sha fama da sabani tsakaninsa da takwaransa a jam’iyyar ta ÖVP Wolfgang Schüssel, musamman saboda amincewar da takwaran nasa yayi ta kafa mulkin hadin guiwa da jam’iyyar FPÖ mai zazzafan ra’ayin kyamar baki a karkashin jagorancin Jörg Haider. Thomas Klestil yayi amfani da ikon da aka tanadar masa domin hana nadin ministoci da dama daga jam’iyyar ta masu kyamar baki. An lura da takaicin dake tattare a zuciyarsa a game da wannan manufa ta hadin guiwa lokacin da yake rantsar da Wolfgang Schüssel a mukaminsa na P/M ba tare da wata murna a fuskarsa ba. To sai dai kuma duk da haka sai da ya gabatar da kiran nuna halin sanin ya kamata lokacin da kasashe 14 na Kungiyar Tarayyar Turai suka tsayar da shawarar mayar da Austriya saniyar ware sakamakon mulkin hadin guiwar da aka kulla tare da jam’iyyar ta FPÖ. Bisa ga ra’ayinsa wannan mataki na takunkumi bai dace ba, inda yake cewar:

Akwai bukatar daukar nagartattun matakai wajen shawo kan masu kyamar wannan manufa tsakanin kawayen namu su 14 domin su janye daga wannan mataki. Zan ci gaba da yin bakin kokarina wajen gudanar da shawarwari da tuntubar juna, amma a ganina a wannan halin da ake ciki bin manufofi na diplomasiyya shi ne mafi alheri bisa manufa.

Klestil ya fuskanci adawa mai tsananin gaske daga ‚ya’yan jam’iyyar FPÖ, kazalika har ma da ‚ya’yan jam’iyyarsa ta ÖVP sakamakon daridarinsa da gwamnatin ta hadin guiwa. Tsofon shugaban na kasar Austriya, wanda ya rasu yana da shekaru 71 da haifuwa, ya bar ‚ya’ya uku da matarsa guda daya.