Rasuwar sarki Abdullah na Saudiya | Labarai | DW | 23.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rasuwar sarki Abdullah na Saudiya

Da sanyin safiyar wannan Jumma'a ne Allah Ya yi wa Sarki Abdullah na kasar Saudi Arabiya rasuwa bayan rashin lafiya. An nada Salman a matsayin sabon sarki.

Gidan talabijin kasar ta Saudiya ya bayyana cewa Sarki Abdullah ya rasu ne ya na da shekaru 90 a duniya bayan 'yar gajeruwar rashin lafiya. Rahotanni sun nunar da cewa sarkin ya sha fama da cutar da take da nasaba da huhu ne na tsahon makwannin gabanin rasuwar tasa.

A yanzu Yarima Salman da ke zaman dan uwa ga marigayi Sarki Abdullah ne za a nada a matsayin sabon sarki.