Rashin tsaro ya sanya direbobi fargaba | Zamantakewa | DW | 30.04.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Rashin tsaro ya sanya direbobi fargaba

A yayin da tabarbarewar tsaro ke ci gaba da zama barazana a Najeriya kungiyoyin direbobin motocin fasinja sun nuna fargabarsu game da irin fasinjojin da suke dauka.

Direbobin sun kuma bayyana irin kalubalen da suke fuskanta a cikin wannan yanayi a sakamakon karuwar tabarbarewar bangeren tsaro dake janyo tashi da fashewar bama-bamai a tashohin mota a Najeriya wanda ke addabar hukumomi da kungiyoyin alummar kasa.

Tuni dai hadaddiyar kungiyar direbobin motocin haya ta kasa ta fito fili karara ta na nuna damuwarta da kuma fargabar da ta ke da shi bisa ga irin wannan munmunan yanayi na fashewar miyagun makamai, to sai dai a wannan karan daukacin kungiyoyin direbobin motocin haya na kasar sun dauki matakan dakile ci gaban farfashewar bama-bamai da sauran makaman dake tarwatsewa suna lakume rayukan alumma da wasu 'yan bindiga ke dana wa a cikin garejin shiga motocin haya dan cimma wani buri kamar dai yadda Alhaji Alhassan Haruna shugaban kungiyar direbobin jihar Kaduna dake Najeriyar ke cewa:

"A nan jihar Kaduna kawai muna da direbobin dake da rejista sama da 50,000 wannan karon jami'an sojojin wannan kasar sun gayyace mu domin nuna mana sababbin dabarun da suka cancanta domin kubutar da al'umma game da irin munanan ayyukan 'yan ta'adda dake hallaka alummar wannan kasar, mu kuma ana mu bangaren muna yin dukkanin mai yiwuwa wajen tabbatar da ganin cewa mun horar da jama'armu dukkanin hanyoyin da suka wajaba kan yadda za su kula da kuma kare rayukan matafiya a duk inda suke."

Mawallafi: Ibrahima Yakubu
Edita: Lateefa Mustapha Ja'afar