Rashin tabbas game da lafiyar gwamnan jihar Taraba | Siyasa | DW | 26.08.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Rashin tabbas game da lafiyar gwamnan jihar Taraba

Bayan da ya shafe watanni goma yana yin jinya a Amirka a sakamakon haɗarin jirgin saman da ya yi, a yanzu gwamna Danbaba Suntai ya koma gida.

Masu yin nazari a kan harkokin yau da kullum a jihar Taraba sun soma hangen wata barazanar kan siyasar jihar, biyo bayan dawowar Gwamnan Danbaba Suntai. Abin da dai ya fito fili shi ne na bambancin addini da 'yan siyasa ke amfani da shi wajen raba kawunan jama'a kamar yadda ya fito fili a garin Jalingo bayan dawowar Gwamnan.

Ruɗani da kuma sanin rashin tabbas a kan dawowar gwamna

Ko shakka babu gwamnan wanda aka dawoda shi ya tarad da jihar cikin wani ruɗani sakamakon jagorancin da mataimakinsa Alhaji Garba Umar ke kai, wanda wasu ke cewar ba ya tafiya yadda aka soma da farko. Alhaji AD Usman mai nazarin al'amura a jihar wanda ya tabbatar mani da cewar dawowar gwamna Suntai na zaman barazana ga jihar da ke fama da rikice-rikicen siyasa da na addini shekaru da dama ya ara da cewar.

Ya ce : ''Dangane da yadda aka dawo da gwamnan ba tare da ya sami lafiya ba , wannan wani abu ne da zai ƙara kawo cikas ga yunƙurin da ake yi, na sauke shi daga muƙamin abin da ya ce an yi amfani da wata manufa ta addini.''

Sa-in-sa tsakanin 'yan siyasar a kan wannan batu

Nigerian President Goodluck Jonathan speaks during a nationwide live broadcast on the state television on May 14, 2013. President Goodluck Jonathan has declared state of emergency in the nation's troubled northeast states of Yobe, Borno and Adamawa, where Islamic extremists now control some of the country's villages and towns, promising to send more troops to fight what is now an open rebellion. AFPPHOTO/PIUS UTOMI EKPEI (Photo credit should read PIUS UTOMI EKPEI/AFP/Getty Images)

Goodluck Jonathan

Sai da fa yayin da Alhaji AD Usman yake wannan kira, tsohon sakataren gwamnatin jihar mai kuma yin biyayya ga gwamna Suntai Ambasada Emmanuel Njiwa cewa yayi babu batun bambancin addini a wannan tafiya. Ya ce : '' Kawai gwamna Ɗanbaba Suntai ya dawo gida ne domin ci gaba da mulkin jihar kamar yadda talakwan suka ɗoramasa nauyi.''

Akwai dai buƙatar mayar da hankali domin zaman fahimta cikin lumana a yanki a daidai wannan lokaci da gwamnan wanda dawowar tasa kamar yadda rahotanni suka tabbatar, babu wani jami'in gwamnatin da yayi tozali da shi, baya ga wata ziyarar ma da gwamnan jihar Adamawa Murtala Nyako ya kawo jihar domin marabtan shi gwamna Suntai ɗin da ba ta yi nasara ba, inda kamar yadda aka tabbabtar cewar gwamna Nyako bai samu saduwa da makwabcin nasa ba.

Mawallafi : Muntaqa Ahiwa
Edita : Abdourahamane Hassane

Sauti da bidiyo akan labarin