Rashin ci gaba a arewacin Afirka ta Tsakiya
March 28, 2013Da ma dai al'umomin yankin arewa maso gabashin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya sun dade suna kokawa game da komabayar da suke fuskanta. Ko da gamayyar Kungiyoyin tawaye ta Seleka da ta kwace mulki, sai da ta zargi gwamnatin Bozize da yi wa yankin rikon sakarnar kashi. Su ma dai masu sa ido a harkokin zabe ba su sami damar isa wannan yanki ba a shekara ta 2011, saboda zama ruwan dare da fashin makamai ya yi. A cewar Adolphe Ngouyombo, shugaban kungiyar kare hakkin bani Adama da taimakon jin kai ta Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, dalilai da dama ne suka jefa wanyin cikin hali da ta ke ciki a yanzu.
"Wannan ya samo tushe ne tun lokacin da kasar ta samu 'yancin kanta daga turawan Faransa. Wannan ya na da nasaba da yanayin yankin. Baya ga nisa, a damuna ba a samun damar shiga ko fita."
Ma'amala tsakanin yankin da Chadi da Sudan
Sai dai kuma yanki na Arewa maso gabashin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya na da iyaka da kasashen Chadi da Sudan da kuma Sudan ta Kudu. Yankin ya yi kaurin suna a sigar fataucin muggan makamai. Kazalika 'yayan wannan yankin da ake damawa da su a harkokin siyasa da ma dai na mulki ba su taka kara sun karya ba. Su na ma daga cikin rukunin wadanda suke da karancin iya karatu da kuma rubutu. Sai dai kuma al'amuran sun fara inganta a shekarun baya-bayannan sakamakon dauki da suke samu daga kungiyoyin jin kai na kasashen waje. Amma kuma ma'amala tsakanin kabilun wannan yanki na nan daram dakam duk kuma da rikicin tawaye da kasar ta saba cin karo da shi. Daidai a cikin gamayyar kungiyoyin tawaye ta Seleka, ana samun 'yayan wannan yankin da ke jin harshe fiye da daya, a cewar Adolphe Ngouyombo
"A kan iyaka dai jama'a na yin magana ne cikin harsuna biyu. A nan ba wai sango da daukacin 'yan jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ke ji ba ne kawai harshen ma'amala. Amma suna magana ma cikin harshen larabci. A yanzu dai abu ne mai matikar wuya a yi bayani game da yawan wannan yani a gamayyar kungiyoyin tawayen Seleka. Amma a bin da ya fito fili daga binciken da na gudanar jiya shi ne cewa akwai musulmai da dama a cikin gamayyar."
Daga Arewa maso gabas Djotodia ya fito
Shi ma dai Michel Djotodia da ya ayyana kansa a matsayin sabon shugaban Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya dan asalin garin Birao da ke wannan yankin ne. Yayin da shi kuma firaminista Nicolas Tiangaye ya fito daga tsakiyar Jamhuriyar afirka ta tsakiya, a cewar Ngouyombo.
"Shugaban dan sasalin yankin Arewa maso gabas ne. Amma dai firaminista ya fito ne daga Gouam da ke tsakiyar kasar musamman ma daga garin Bouca."
Gaggwarmaya da Tiangaye ya ke yi wajen kare hakkin bani Adama da kuma mutunta yarjejniyar zaman lafiya da gwamnati da 'yan tawaye suka cimma a Libreville na daya daga cikin dalilan da suka sa aka bai wa firaministan damar ci gaba da rike wannan mukami na firaminista a Jamhuriyar Afirka ta tsakiya.
Rahoto cikin sauti na kasa
Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Mohammad Nasiru Awal