Rashin bai wa ′yan jarida kariya a Equatorial Guinea | Labarai | DW | 01.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rashin bai wa 'yan jarida kariya a Equatorial Guinea

Hukumomi a Equatorial Guinea sun ba da umarnin hana sayar da jaridar Ebano da ke a matsayin jaridar gwamnati mai fitowa a mako-mako dangane da wallafa batun rishin bai wa 'yan jarida kariya a kasar.

Samuel Obiang Mbana

Samuel Obiang Mbana wakilin DW a Equatorial Guinea

Ita dai jaridar ta Ebano ta wallafa hiran da ta yi da 'yan jaridu masu zaman kan su da suka hada da wakilin kanfanin dillancin labaran kasar Faransa na AFP, da wakilin Afrika N°1, da kuma wakilin radio DW a wannan karamar kasa ta Tsakiyar Afirka. Cikin hiran 'yan jaridar sun ce 'yan jaridan gwamnati tamkar suna cikin kaso ne domin ba sa iya fadar albarkacin bakinsu sai kawai abun da gwamnati ta ke bukata.

Wata majiya ta ofishin ministan yada labaran kasar ce dai ta sanar cewa, ministan ne da kan shi ya bada wannan umarni janye dukannin jaridar ta Ebano da aka soma sayar wa. Tuni dai masu lura da al'ammura ke kallon wannan mataki na gwamnati ta Equatorial Guinea a matsayin wani abun da ya tabbatar da zargin da 'yan jaridar ke yi wa magabatan.