Rashin amicewa da sojojin Farasana a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya | NRS-Import | DW | 21.08.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

NRS-Import

Rashin amicewa da sojojin Farasana a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

Dubban jama'a suka gudanar da gangami a birnin Bangui domin neman ganin sojojin Faransa sun fice daga ƙasar.

Masu aiko da rahotannin sun ce duk da ruwan sama kamar da bakin Ƙwarya da aka riƙa yi a birin, jama'ar sun yi jerin gwano tun daga anguwar PK5 har zuwa cibiyar rundunar sojojin kiyaye zaman lafiya ta MDD wato MUNISCA.

Suna raira kallamun suka ga shugaba Francois Hollande saboda zargin da suke yi wa sojojin na Faransa da galazawa musulmi. Wannan gamgami ya biyo bayan wata arangama da aka sha a kwanaki biyun da suka wuce, tsakanin musulmin da sojojin na Faransar waɗanda ke ƙoƙarin ƙwace makamai daga hannu jama'a .

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Mouhamadou Awal Balarabe