Rasha za ta fuskanci karin takunkumi | Labarai | DW | 14.04.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rasha za ta fuskanci karin takunkumi

Kungiyar Tarayyar Turai na tattauna yiwuwar kakaba wa Rasha sabbin takunkumai karya arziki kan abun da ta kira rura wutar rikicin Ukraine da mahukuntan Moscow ke yi.

Ministocin harkokin kasashen waje na kungiyar sun yi zargin cewa Rasha ce umul'aba'isan duk tashin hankalin da ake fama da shi yanzu haka a gabashin Ukraine. Ministocin kasashen ketare na Birtaniya William Hague da takwaransa na Faransa Laurent Fabius sun ce dole ne su dauki tsauraran matakai a kan Rasha domin kuwa ita ce ke iza wutar daga bayan fage.

Wannan matakin nasu dai na zuwa ne a dai dai lokacin da shugaban gwamnatin rikon kwaryar Ukraine din ya bukaci Majalisar Dinkin Duniya ta kai dauki na dakarun wanzar da zaman lafiya a gabashin kasar domin shawo kan rikicin. A hannu guda kuma Rashan dake ci gaba da musanta zargin da Ukraine da kwayenta kasashen yamma ke mata na iza wutar rikicin ta ce, duk wani mataki na karfi da mahukuntan Kiev din za su dauka a kan 'yan awaren wani abu ne da ka iya haddasa yakin basasa a kasar.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Mouhamadou Auwal Balarabe