Rasha ta zargi Jamus da bata mata suna
April 4, 2014Ministan kudin na Jamus Wolfgang Schäuble dai ya bayyana mamayar da Rashan ta yi wa yankin Kirimiya na Ukraine a matsayin irin ayyukan da Adolf Hitler ya yi gabanin yakin duniya na biyu a yayin da yake jawabi ga wasu yara 'yan makaranta. Ita ma dai shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta bayyana matakin Rashan a yankin Kirimiya da wani abu da ya sabawa dokokin kasa da kasa. A hannu guda kuma ministocin harkokin kasashen ketare na kungiyar EU za su fara wani taro na yini biyu inda ake sa ran batun yankin Kirimiya ne zai mamaye tattaunawar tasu. Taron nasu dai na zuwa ne kwana guda bayan da shugaban Amirka Barack Obama ya sanya hannu kan amincewa da baiwa Ukraine bashin dalar Amirka biliyan daya.
Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Zainab Mohammed Abubakar