SiyasaTurai
Ana rigima da Rasha kan sararin samaniya
November 16, 2021Talla
Wannan ya biyo bayan zarge-zargen da kungiyar tsaro ta NATO da Amirka suka yi mata cewa, ta tsokalo tartsatsin tauraran dan Adam da zai yi wa samaniya lahani. To amma a martanin da Rashan ta fitar ta musanta hakan, tana mai cewa ba kanta farau ba domin kasashen Indiya da Chaina ma sun taba yin haka a shekarun baya. Ministan Harkokin Wajen Rashan Sergei Lavrov ya siffanta zargin da Amirka ke yi a matsayin abin da bai dace ba.
Sai dai sakatare janar na kungiyar tsaro ta NATO Jens Stoltenberg ya ce babu wani kame-kame, wauta ce kawai Rasha ta yi da sunan gwajin makami a sararin samaniya.