Rasha ta musunta cimma yarjejeniya da Ukraine | Labarai | DW | 03.09.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rasha ta musunta cimma yarjejeniya da Ukraine

Rahotanin da ke yin karo da juna na nuna cewar ƙasashen Ukraine da Rasha sun samu ci gaba a ƙoƙarin da ake yi na tsagaita buɗe wuta a gabashin Ukraine.

Tun da farko fadar gwamnatin Ukraine ta ba da sanarwar cewar an cimma wata yarjejeniyar dakatar da buɗe wuta ta tsakanin shugaba Vladmir Putin da Petro Poroshenko.

Kafin daga bisiani kakakin shugaban ƙasar Rashar ya ƙaryata sanarwa kan cewar Rasha ba ta cikin yaƙin. Amma kuma ya amince cewar shugabannin biyu na Rasha da Ukraine sun tattauna ta wayar tarho waɗanda kusan dukkaninsu suke da ra'ayi guda wajen kawo ƙarshen tashin hankali na gabashin Ukraine.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu