Rasha ta bawa Snowden mafakar siyasa
August 1, 2013Rahotanni daga birnin Moscow kasar Rasha na cewar dan Amirkan nan Edward Snowden da ya kwarmata wasu bayanan sirrin Amirka, kuma ya ke makale a filin jirgin saman Moscow din na sama da wata guda ya samu mafakar siyasa ta shekara guda a kasar.
Da ya ke bayani game da wannan batun, lauyan Mr. Snowden din Anatoly Kucherena ya ce a wannan Alhamis din ce ya mikawa Snowden din takardun izinin zama a kasar na wucin gadi bayan da hukumomin kasar suka amince da bukatar da ya mika musu a kwanakin baya.
Wani jami'i da ke aiki a filin jirgin saman da ke Moscow din inda Snowden ya makale ya gayawa kamfanin dillancin labarai na Reuters a Moscow cewar ya shaida sanda Snowden din ya bar filin jirgin saman sai dai lauyansa ya ce ba za su bayyana inda ya nufa ba saboda dalilai na tsaro.
Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Umaru Aliyu