Rasha na goyon bayan shirin tattaunawa a Syriya | Labarai | DW | 03.02.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rasha na goyon bayan shirin tattaunawa a Syriya

A karon farko ministan harkokin waje na Rasha Serguei Lavrov ya gana da jagoran yan addawa na Syria wanda ya gargaɗa da su soma tattaunawa da gwamnatin Bashar Al Assad

Ƙasar Rasha ta ce ta na goyon bayan ci gaba da tutunɓar juna tare da yan tawayen Syriya tare da gargaɗa su da su soma gudanar da tattaunawa da gwamnatin.A wata ganawa da ya yi a jagoran yan adawar a birnin Munich a tsaron kula da tsaro na ƙassa da ƙasa Ahmed Moaz El Khatib a karon farko.

Ministan harkokin waje na ƙasar ta Rashar Serguei Lavrov ya ce a kwai buƙatar ɓangarorin biyu su zauna kan tebrin shawarwari.Sannan mataimakin shugaban Amurka Joe Biden da ministan harkokin wajan na Rashan su dukanin su, sun amince su yi aiki tare a kan batun na Syrya du kuwa da saɓannin da ke tsakanin ƙasashen a kan batun.Tuni dai da gwamantin Amurka ta ba da sanarwa cewar ba zata baiwa yan tawayen na Syriya makamai ba.

Mawallafi: Abdourahamane Hassane
Edita : Halima Balaraba Abbas