Rasha na fuskantar kalubalen tsaro | Labarai | DW | 30.12.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rasha na fuskantar kalubalen tsaro

Hare-haren kunar bakin wake sun sako kasar Rasha a gaba, gabanin bikin gasar wasannin guje-guje da tsalle-tsalle na lokacin hunturu.

A kalla mutane 10 ne suka rasa rayukansu sakamakon wani sabon harin kunar bakin wake da aka kai a wata mota kirar Bus a birnin Volgograd na kasar Rasha dake zaman karo na biyu a tsahon yini biyu.

Harin dai ya zo ne kwana guda bayan da wani harin kunar bakin waken da aka kai a babbar tashar jiragen kasa dake kudancin kasar ya yi sanadiyyar mutuwar a kalla mutane 17.

Duka wannan na zuwa ne kwanaki 40 gabanin gasar wasannin guje-guje da tsalle-tsalle na lokacin hunturu, da ake wa lakabi da Winter Olympics wanda kuma za a gudanar a Rashan.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Saleh Umar Saleh.