1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasa rayuka a Bangaladesh sakamakon siyasa

Zulaiha Abubakar
December 30, 2018

Akalla mutane 12 sun rasa ransu a kasar Bangaladesh sakamakon rikici tsakanin 'yan jam'iyya mai mulki da bangaren adawa a lokacin da al'ummar kasar ke tsaka da gudanar da zabe.

https://p.dw.com/p/3Ammm
Bangladesch Dhaka Polizei sichert Vorbereitungen für Parlamentswahl
Hoto: Imago/Zumapress/K. Salahuddin Razu

Jami'an 'yan sanda sun yi nasarar harbin uku daga cikin wadanda suka tada rikici bayan sun hallaka dan sanda guda. Alamu na nuni da cewar Firaminista Sheikh Hasina za ta iya samun nasarar ci gaba da rike mukaminta a karo na hudu

Sai dai duk da samun yabn da Firaministar ke samu daga ciki da wajen kasar sakamakon farfado da tattalin arzikin kasar da kuma karbar 'yan gudun hijira daga kasar Myanmar, masu hamayya da mulkinta na zarginta da hana adawa a fadin albarkar baka a fadin kasar.

A nata bangaren hukumar zaben kasar ta bayyana cewar idan bincike ya tabbatar da samun aringizon kuri'u kamar yadda 'yan adawa suka zarga, babu shakka hukumar za ta dauki matakin da ya dace.