Rantsar da wakilan kotun tsarin mulki a Nijar
March 25, 2013
Kotun tsarin mulkin kasar ta Nijar ta kunshi mambobi bakwai wadanda suka hada da wakilin shugaban kasa da na fadar shugaban majalisar dokoki da na kungiyar malaman jami'a da na kungiyoyin farar hula da ke fafatukar kare hakkin bil Adama a Nijar. Sai kungiyar lauyoyi wadda ke da wakilcin mutun guda sai kuma ta alkalai dake da wakilai biyu, Bayan an rantsar da su a bisa littafin addinin ko wane daga cikinsu.
Bikin kaddamar da mambobin kotun tsarin mulkin ya samu halartar
jakadun kasashen waje da ke aiki a Nijar da 'yan majalisar dokoki da wakillan kungiyoyin farar hula da na jam'iyyun siyasa. Da suke tsokaci kan wannan sabuwar kotun tsarin mulki kawancen jam'iyyun adawa na ARN ta bakin kakakinsa Malam Lawal Amadu bayyana fata ta yi na ganin kotun za ta zare gaskiya cikin aikinta. To amma daga nashi bangare Dr Naray daya daga cikin mambobin kotun tsarin mulkin da aka rantsar fata ya yi Allah Ya kama masu su iya kai wadannan kaya da suka dauka.
A nan gaba mamboobin kotun za su zama na musamman domin zaban shugaba da mataimakinsa daga cikinsu.
Mawallafi : Gazali Abdu Tasawa
Edita : Zainab Mohammed Abubakar