1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Neman mafita daga rigingimu da suka addabi duniya

September 21, 2021

Bikin na bana ya zo a daidai lokacin da harkokin tsaro ke kara dagulewa a Najeriya, inda ake zaman tankiya tsakanin kabilu da addinai gami da hare-haren 'yan tarzoma da masu garkuwa da mutane.

https://p.dw.com/p/40cw7
Jerin gwanon 'yan makaranta don neman zaman lafiya a kasar Mozambik
Jerin gwanon 'yan makaranta don neman zaman lafiya a kasar MozambikHoto: DW/D. Anacleto

Ranar 21 ga watan Satumbar wannan shekara rana ce da Majalisar Dinkin Duniya ta ware domin yin bikin ranar zaman lafiya a wani kokari na nemo mafita kan tashe-tashen hankula da ake fama da su a fadin duniya. Sai dai bikin na bana na zuwa ne a daidai lokacin da harkokin tsaro ke kara dagulewa a Najeriya, inda ake zaman tankiya tsakanin kabilu da addinai gami da hare-haren kungiyoyin 'yan ta'adda da 'yan bindiga masu garkuwa da mutane.

A tarayyar ta Najeriya dai akwai yankunan da sun manta da samun zaman lafiya, inda a kullum ake samun asarar rayuka saboda tashe-tashen hankula na addini da kabilanci da na neman iko ko neman mallakar wani kaso na tattalin arzikin kasa.

Yaduwar makamai a hannun jama'a na daga cikin dalilan da ke rura wutar rikice-rikice
Yaduwar makamai a hannun jama'a na daga cikin dalilan da ke rura wutar rikice-rikiceHoto: Audu Ali Marte/AFP/Getty Images

Wani rahoto da wata cibiyar tsaro ta fitar a wannan watan na Satumba ya nuna cewa a cikin watan Agusta an hallaka mutane 698 a sassan Najeriya.

Banda hare-hare 'yan Boko Haram da ISWAP a shiyyar Arewa maso gabashin Najeriya da na 'yan bindigar daji a yankin Arewa maso yammaci da tsakiyar Arewacin, ana kuma samun tashe-tashen hankula na kabilanci da na addini a kusan dukkanin sassan kasar.

Masana da masharhanta na ba da irin na su dalilan da abin da ya hana a samu zaman lafiya a Najeriya tsawon lokaci.

Yayin da ake laluben hanyoyin da za a samo bakin warware matsalolin da ke haifar da zaman lafiya masana da masharhanta gami da shugabannin al'umma da na addini sun ba da shawarwarin abin da ya kamata a yi.

Yayin da wasu da dama ke ganin ya zama dole a dakile hanyoyin da ake safarar haramtattun makamai da su ma wanzuwarsu tsakanin al'umma na rura wutar akwai kuma masu ganin sai ana hukunta wadanda aka samu da laifukan kunna wutar rikici in ana son samun zaman lafiya.