Ranar yancin yan jarida | Labarai | DW | 03.05.2006
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ranar yancin yan jarida

Cibiyar nazarin aikin jarida na kasa da kasa ,ta bayyana cigaban kisan gilla da akewa yan jarida a sassa daban daban na duniya bawai masifa ne kadai wa iyalansu ba,amma wata kaface da ake danne muhimman labarai a kasashen da ake gudanar da mulki irin na democradiyya.A sakon da da ta gabatar dangane bukin ranar yancin yan jarida ta dinya dake gudana a yau,cibiyar wadda ke fafutukan kare yancin yan jarida wadda keda matsuguninta a birnin Vienna,ta bayyana kisan gilla da akayiwa yan jarida 65 a shekarar data gabata kadai da kasancewa babban balai a wannan aiki,wanda ke tunasar da irin barazana da yan jarida da kuma yan jarida masu daukan hoto ,ke ciki,da irin kalubale da suke fuskanta.Cibiyar ta bayyana irin wadannan kisan gilla da kasancewa babbar asara wa aikin,kana a hannu guda kuma yana hana alummomi sanin labarai dangane da halin da ake ciki na gaskiya.musamman ma a gangane da muhimman batutuwa da suka hadar da rashawa da cin hanci na gwamnatoci da zame ruwan dare a kasashe.Adangane da hakane kungiyar kare hakkin yan jaridan ta jaddada bukatar binciken wadanda keda alhakin ire iren wadannan kisan gillan ,domin daukan matakai na hukunci.

 • Kwanan wata 03.05.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammad
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/Bu6h
 • Kwanan wata 03.05.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammad
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/Bu6h