1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwaNa duniya

Ranar tuni da kare hakkin masu neman jinsi

Mouhamadou Awal Balarabe
May 17, 2024

A ina ne ake kare hakkin masu neman jinsi? Shin masu neman jinsi suna samun kariyar da ta dace? binciken hukumar kare hakkin bil Sdama na tarayyar Turai ya bayar da amsar wadannan tambayoyi.

https://p.dw.com/p/4g11C
ILGA Europe March in Brüssel Homosexuelle Rechte
Hoto: Joel Le Deroff/ILGA

Hukumar kare hakkin bil'adama ta Turai ta fitar da jerin kasashen nahiyar da suka fi kare hakkin 'yan luwadi da madigo, a daidai lokacin da a ranar Jumma'a 17 ga watan Mayu ake tuni da ranar yaki da cin zarafin masu neman jinsi. Wannan taswirar ta nunar da cewar kasar Malta ce 'yan luwadi da madigo ke fuskantar karancin barazana a nahiyar Turai.

Taswirar da ke dauke da launin bakan gizo, wacce aka shafe tsawon shekaru 11 ana wallafawa, ta nuna matsayin kariyar da masu neman jinsi ke samu a fannin doka a duk fadin Turai. Kungiyar ILGA reshen Turai ce ta fitar da darajar kowace kasa, bisa la'akari da kayyadaddun ka'idoji ciki har da daidaiton hakki tsakanin 'yan luwadi da madigo da sauran al'umma, da kuma kariya daga muzgunawa da kiyayya da wariya da suke fuskanta, hadi da yadda zamantakewar masu neman jinsi ke kasancewa a cikin 'yan uwa da dangi.

Sumbatar juna ta masu neman jinsi  Beljiam
Sumbatar juna ta masu neman jinsi BeljiamHoto: Bernd Riegert/DW

Tsibirin Malta ya sake kasancewa a kan gaba na kasashen da suka fi kare hakkin 'yan luwadi da madigo, inda ya samu maki 88 cikin 100, yayin da Iceland ke a matsayi na biyu a bana da maki 83. Rukunin kasashen da ke kan gaba a Kungiyar Tarayyar Turai kuwa sun hada da Beljiyam da Luxembourg da Spain da Denmark da Finland da kuma Girka, inda kowacce ta samu maki 70. A takaice dai, kasashen arewaci da yammacin Turai ne suka fi samar da kyakkyawan yanayin kare 'yan LGBTQ+. A daya bangaren kuwa, Rasha da Azerbaijan da Turkiyya sun mamaye jerin kasashen da ke da karancin mutunta hakkin maza masu neman maza da mata masu neman mata. A cikin Kungiyar Tarayyar Turai kuwa, Poland ce ta kasance a matsayi na baya-baya da maki 17 bayan shekaru goma na mulkin jam'iyyar PiS mai ra'ayin mazan jiya.

A Italiya ma, yanayin masu neman jinsi ya kara tabarbarewa bayan da kawancen masu tsattsauran ra'ayin rikau na Fratelli da Lega da Forza suka karbi ragamar mulkin kasar. Italiya ta kasance a cikin rukuni na uku na kasashen EU tsawon shekaru saboda yawancin tanade-tanaden doka game da zaman iyali da kuma auren jinsi suna tafiyar hawainiya, in ji Katrin Hugendubel, darektar sashen shari'a a ILGA.

Kungiyar LGBTQ ta masu neman jinsi a Turkiyya
Kungiyar LGBTQ ta masu neman jinsi a TurkiyyaHoto: Dilara Senkaya/REUTERS

"Yayin da wasu kasashe ciki har da Jamus suka rigaya suka ci gaba, a wasu kasashe da dama ana samun koma baya, wanda ke nufin cewar ba a fitar da wasu sabbin dokoki don kare masu neman jinsi ba. Muna ganin yadda kiyayya da muzguna wa 'yan luwadi da madigo ke karuwa, inda wasu gwamnatoci ke kara ta'azzara tauye hakkin dan Adam, musamman na masu neman jinsi, wannan yana da matukar hadari."

A cewar lauyar kungiyar ILGA Katrin Hugendubel, martabar kasashen Turai a fannin kare hakkin masu neman jinsi da kyar ta canza saboda da babu wani yunkuri da ya rage don tabbatar da hakkin dan Adam a cikin doka. Amma dai Jamus ta fita zakka, inda majalisa ta albarkanci dokar da ke bai wa kowa izinin zabar jinsin da yake so. Irin wannan ci-gaban, ana samun shi ne a cikin kasashen 11 daga cikin kasashen Turai 49 da aka bincika.

Hukumar kare hakkin bil'adama ta Tarayyar Turai ta gabatar da wani cikakken nazari a ranar yaki da cin zarafin 'yan luwadi, inda ta so sanin yadda wadanda abin ya shafa ke kallon halin da suke ciki. Mutane 100,000 a fadin Turai ne suka shiga wani bincike ta yanar gizo. An gano cewar an fi tattauna batun neman jinsi a makarantu fiye da shekaru biyar da suka gabata, amma a daya hannun kuwa, wariya da cin zarafi da kalaman kiyayya sun karu a rayuwar yau da kullum ta 'yan luwadi da madigo. Fiye da kashi daya cikin goma na 'yan LGBTQ+ ne aka kai wa mummunan hari a kasashen Turai, lamarin da ya zarta alkaluman shekaru biyar da suka gabata,in ji Miltos Pavlou daga hukumar kare hakkin Bil Adama ta Turai da ya jagoranci binciken.

Zorana Mirović ta kungiyar LGBTQ+ a kasar Sabiya
Zorana Mirović ta kungiyar LGBTQ+ a kasar SabiyaHoto: Jelena Djukic Pejic/DW

"Mun iya ganin cewa budewar idanu ya karu. Masu neman jinsi sun fi bayyana kansu a yadda suke. Suna alfahari da gudunmawar da suke bayarwa a tsakanin al'umma. Amma matasa sun fi fuskantar tashin hankali da tsoratarwa. Muna fatan Hukumar EU za ta yi amfani da sabbin dokoki don yaki da wannan dabi'a."

A game da tambayar da ta shafi sanin ko 'yan luwadi da madigon na Turai na kai rahoto ko shigar da kara kan kiyayya ko wariya da ake nuna musu kuwa, amsa ta bambanta daga wannan kasa i zuwa wancan.  A kasar Hungari ga misali, babu dokar da ta halarta auren jinsi, amma kuri'ar jin ra'ayin jama'a ta nunar da cewar sama da rabin 'yan kasar na goyon bayan irin wannan aure.