1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ranar ma'aikata: Halin da ma'aikata ke ciki

May 1, 2013

A yayin da ake bikin ranar ma'aikata a sassa daban daban na duniya, gwamnatin Najeriya na shirin korar ma’aikatan kamfanin samar da wutar lantaraki kimanin dubu ashirin.

https://p.dw.com/p/18QBr
1. Mai, Tag der Arbeit. Die Nigerianische Gewerkschaft NLC. 01.05.2013, Abuja Nigeria Copyright: DW via Yahouza Sadissou, Hausa Redaktion
Hoto: DW

Wannan batu na yunkurin korar ma'aikatan kamfanin samar da wutar lantarki na Najeriya dubu ashirin daya daga hankalin daukacin ma'aikatan wadanda ke cikin jiran a biyasu daukacin hakkokinsu kafin mika kamfanin a hannun yan kasuwa, yunkurin da suke ganin dabara ce ta hana wadanan ma'aikata samun hakkokinsu da a baya aka yi masu alkawari.

Malam Muazu Musa na kungiyar ma'aikatan wutar lantarki ta Najeriya yace duk wani ikirari a kan wannan batu ba zai sa su amince ba har sai lokacin da suka kai ga samun kudaddensu a hannu.

Sannan cewar a watan Febrairu ne gwamnatin Najeriya ta sanar da samar da Naira bilyan 384 da kudaden biyan daukacin ma'aikatan, amma daga baya aka ji wannan bayani na kora daya daga hankalin ma'aikata. To sai dai mai baiwa ministan kula da wuta lantarkin shawara a fanin yada labaru Kande Daniel ta ce babu batun korar ma'ikata.

1. Mai, Tag der Arbeit. Demonstration. 01.05.2013, Zinder, Nigeria Copyright: DW via Yahouza Sadissou, Hausa Redaktion
zanga-zangar ma'aikata a Zinder- NijarHoto: DW

To sai dai kungiyar kwadagon Najeriya ta ce duk wani tabbaci da gwamnati za ta bayar na zaman sai sun gani a kasa, inda kungiyar ta bayyana fushinta a fili da ma kurarin cewar ba zata lamunci take hakin duk wani ma'aikacin kamfanin wutar lantarkin Najeriya da ake shirin kamala mika shi a hannun yan kasuwa ba. Comrade Abbayo Toro shine sakataren da ke kula da sasanta ma'aikatau na kungiyar kwadagon Najeriya.

Batun sayar da kamfanin wutan lantarki Najeriya da tuni aka rarraba shi na zama abin da ke haifar da tada jijiyar wuya a tsakanin ma'aikata da gwamnati saboda tsoron da suke na kauce wa abin da ya faru da ma'aikatan kamfanin sadarwar Najeriyar na Nitel da aka bar wasunsu basu ga tsuntsu basu ga tarko. Maikatan Najeriya dai na daga cikin wadanda ke a baya a fanin kare hakokinsu, abin da ke sanya yiwa aikin daukar sakaka a kasar.

( Ana iya sauraron sauti daga kasa)

Mawallafi : Uwais Abubakar Idris
Edita : Zainab Mohammed Abubakar