Ranar farko ta zaman makokin Mandela | Labarai | DW | 08.12.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ranar farko ta zaman makokin Mandela

Miliyoyin 'yan kasar Afirka ta Kudu sun gudanar da addu'oi a Masallatai da Majami'u da sauran guraren ibada, domin tunawa da gudunmawar da tsahon shugaban kasar marigayi Nelson Mandela ya bayar wajen gina ta.

Yayin addu'oin da suka gudanar, al'ummar kasar ta Afirka ta Kudu sun bayyana alhininsu inda suka ce za su ci gaba da tunawa da Mandela a matsayin uban kasa kuma gwarzo da ya yi gwagwarmayar kwatar 'yanci, sannan kuma mai yafiya babban abin koyi ga kasashen duniya baki daya, wajen kyawawan dabi'u da sulhunta al'umma.

A jawabinsa yayin addu'oin, shugaban kasar ta Afirka ta Kudu mai ci yanzu, Jacob Zuma ya bayyana cewa rashin Mandela ba karamin gibi bane a kasar baki daya.

Mandela dai na zaman shugaban kasar bakar fata na farko, wanda ya yi yaki domin kwato 'yancin bakaken fata da kuma yin gwagwarmaya domin ganin an yiwa kowanne dan kasar adalci.

Shugabannin kasashen duniya da dama da suka hadarda Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon, na daga cikin wadanda za su halarci bukukuwan jana'iza da kuma zaman makoki na tsahon mako guda da za a gudanar a Afirka ta Kudun.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Umaru Aliyu