Ranar ƙarshe ta tattaunawa a Geneva | Labarai | DW | 31.01.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ranar ƙarshe ta tattaunawa a Geneva

Yazuwa yanzu babu dai abin da taron tsakanin wakilan gwamnatin Siriya da na 'yan adawa ya cimma a ƙarƙashin jagorancin babban mai shiga tsakani na Majalisar Ɗinkin Duniya Lakhdar Brahimi.

Bisa ga dukkan alamu dai a tsawon kwanakin da aka yi ana yin taron an gaza samun daidaituwar baki tsakanin sassan biyu a kan maganar dakatar da buɗe wuta da yi war kafa gwamnatin wuccin gadi da kuma isar da kayan agaji.

Mista Brahimi ya ce wannan ganawa da aka yi a karon farko ta gaba da gaba tsakanin ɓangarorin biyu na Siriya masu gaba da juna wata nasara ce. Kuma ya ce tattaunawar da za a yi a yau za ta ƙara zama darasi a garesu na tunanin samun mafita a zagaye na biyu na shawarwarin da za a tsaida ranar nan gaba a yau. A sa'ilin wata ziyara da ya kawo a birnin Berlin na nan Jamus domin ganawa da shugabar gwamnatin Angela Merkel babban sakatran na MDD Ban Ki Moon ya yi tsokaci a kan taron. Ya ce: ''shawarwarin da ake yi a Geneva na gamuwa da cikas da kuma sarƙaƙiya amma muna ci gaba da sa ran cewar za a samu nasara kuma abin da ya fi damun shi ne maganar kai kayan agaji da kuma sakin fursunan siyasa.''

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Usman Shehu Usman