1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kungiyar Afirka za ta kawo karshen rikici a nahiyar

Suleiman Babayo
February 10, 2020

Taron kolin shugabannin Afirka da ya gudana a birnin Addis Ababa na kasar Habasha ya ci alwashin kawo karshen rikice-rikicen da nahiyar ke fuskanta tare da karfafa kasuwanci a tsakanin kasashen.

https://p.dw.com/p/3XYzr
Äthiopien Addis Abeba Gipfeltreffen der Staatschefs der Afrikanischen Union
Hoto: picture-alliance/AA/Palestinian Prime Ministry Office

Shugaban Afirka ta kudu Cyril Ramaphosa wanda ya karbi ragamar shugabancin karba-karba na kungiyar na shekara guda daga hannun Shugaba Abdel Fattah al-Sisi na Masar ya bayyana manufofin da zai bai wa fifiko da suka hada da bunkasa kasuwanci tsakanin kasashen nahiyar gami da kawo karshen rikice-rikicen da ke yaduwa cikin nahiyar ta Afirka:

"Taron da muke yi zai dauki mataki na zahiri dole mu dakile tashe tashen hankala da magance ta'addanci da ke faruwa a kasashe da yankuna, kamar na Sahel da yanzu ke yaduwa zuwa wasu sassan kudancin Afirka."

Äthiopien AU-Gipfel in Addis Abeba | Cyrial Ramaphosa übernimmt Vorsitz von Abdel Fattah al-Sisi
Sabon shugaban AU Ramaphosa da al-SisiHoto: AFP/M. Tewelde

Shugaba Cyril Ramaphosa ya ba da misali da kasashen Sudan ta Kudu da Libiya a matsayin wuraren da zai mayar da hankali domin ganin an samu zaman lafiya. A nasa bangaren babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, António Guterres yace dole nahiyar ta tashi tsaye a bangarori dabam-dabam da gina tsari mai dorewa musamman ganin yadda duniya ke fuskantar sauyin yanayi.

"Dumamar da duniya ke yi lamarin ya nunka a Afirka fiye da sauran yankuna. A shekarar da ta gabata an gamu da bala'oi na guguwa mai karfi da ambaliyar ruwa a kasashen Sahel zuwa Zambiya, haka daga Kenya zuwa Madagaska. Sauyin yanayi na da nasaba da fari masu haifar da asara a kasashen yankin gabashin Afirka."

COP25 25. UN-Klimakonferenz in Madrid | Antonio Guterres
Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio GuterresHoto: AFP/C. Quicler

Wani abin da aka duba shi ne hanyoyin da kasashen Afirka za su shawo kan matsaloli cikin gida da iya samar da kudin da ake bukata wajen tafiyar da dakarun kiyaye zaman lafiya. Rahoton wata kungiya mai zaman kanta da ke bincike kan rikice-rikice ta nuna cewar kasashen na Afirka za su biya kimanin kashi 75 cikin 100 na kudin tafiyar da dakarun kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a nahiyar.

Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Human Rights Watch ta ce shugaban na Afirka ta Kudu ya dauki matsayin a lokaci mai tsauri duba da tashe-tashen hankula da ake fuskanta da ke janyo tauye hakkin jama'a.