Ramaphosa ya yi rantsuwar kama aiki | Labarai | DW | 25.05.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ramaphosa ya yi rantsuwar kama aiki

Akalla mutane dubu 35 ne suka hallara a bikin rantsar da  Cyril Ramaphosa a matsayin shugaban kasar Afirka ta Kudu

Sabon shugaban kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya yi rantsuwar kama aikin ne a gaban shugabannin gwamnatocin kasashen Afirka da dama. Bikin rantsuwar wanda ya gudana a Pretoria babban birnin kasar, an shirya 'yan sanda dubu 25 don tabbatar da tsaro.

A cewa  Khusela Diko kakakin shugaban kasar, a lokacin kama rantsuwa Shugaba Cyril Ramaphosa zai tabo batun hadin kan kasa da samarwa matasa aikin yi da kuma farfado da martabar kasar a matsayin wacce ke fada a ji a harkokin nahiyar Afirka. Mai shekaru 66 a duniya, Ramaphosa  ya kasance mataimakin shugaba Jacob Zuma tun a shekara ta 2014, sai dai akwai babban kalubale da ke jiransa musamman rashin aikin yi da kuma yakar cin hanci da rashawa.