Ramaphosa ya koma gida saboda rikici
April 20, 2018Talla
Shugaba Ramaphosa da ya karbi mulki a watan Fabrairu bayan ya sha alwashi na farfado da tattalin arzikin kasa da murkushe ayyukan masu cin hanci da rashawa ya ce zanga-zangar da ke wakana a lardin Arewa Maso Yamma na kasar inda ake gwabzawa da 'yan sanda lamari ne da zai yi illa ga kasar don haka sai ya yi kira da kwantar da hankula a koma tattaunawa.
Ramaphosa ya dai yi kira ga 'yan sanda su yi taka tsantsan kar a yi amfani da karfi da ya wuce kima yayin da masu zanga-zanga suka farwa shaguna suna dibar kayan jama'a a wannan zanga-zanga da ke da nasaba rashin aikin yi da tsadar gidaje da karuwar cin hanci da rashawa a kasar. Lamarin dai na nuna babban kalubale da ke gaban sabon shugaban.