Rahoton shekara na RSF | Siyasa | DW | 30.12.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Rahoton shekara na RSF

Ƙungiyar ´yan jarida ta ƙasa da ƙasa, ta bayyana rahoton shekarar 2010 game da aikin ´yan jarida a duniya

Tutar Reporter sans Frontière

Tutar Reporter sans Frontière

Rahoton shekara-shekara na ƙungiyar da ke da rajin kare haƙƙin 'yan jarida wato Reporters Sans Frontiéres(RSF), ya ce yawan 'yan jaridan da suka rasa rayukan su a bakin aiki ya ragu bisa abun da aka samu a bara da kashi 25 bisa 100. Lamarin da kuma ya shafi duk nahiyoyin duniya, amma abun da yafi ɗaukar hankali, shine ƙaruwar da aka samu a yawan garkuwa da ake yi da 'yan jaridun ana kuma neman kuɗin fansa. Pinado Abdu na ɗauke da ƙarin bayani.....

Aƙalla 'yan jarida 57 ne suka rasa rayukan su a bakin aiki a shekarar 2010, bisa ga ƙiyasin rahoton da ƙungiyar ta Reporters Sans Frontiéres ta wallafa bana, wanda ya nuna cewa an sami raguwa 79 da suka rasa rayukan su a shekarar 2009. A yayin da aka yi garkuwa da 51 daga 33 da aka gano a bara. Jami'an tsaro sun kama 535 wasu 1374 sun fuskanci azabtarwa, an kuma taƙaita wa kafafen yaɗa labarai fiye da 500 'yancin yaɗa labarai, sannan yan jaridan 127 sun tsere daga ƙasashen su.

A wata sanarwar da ƙungiyar ta RSF ta fitar, Jean Francois Julliard babban sakataren ƙungiyar ya ce abun mamaki ne ganin cewar mutane kaɗan ne suka rasa rayukan su a filin daga a shekarun baya-bayan nan musamman ma a ƙasahen Somaliya da Iraƙi inda suke fama da hare-hare da tashe-tashen hankula, kuma a saboda haka ne suke ganin cewar 'yan jarida a yanzu suna rasa rayukan su ne a hannun 'yan ta'adda amma ba a wuraren da ake fama da yaƙi ba.

Tun da ƙungiyar ta RSF ta fara wallafa irin wannan rahoton, wannan ne karo na farko da take sanya alamar tambaya bisa yadda alƙalkuman ke nuni da yawaitan yin garkuwa da 'yan jaridan, domin a shekarar 2008 an yi garkuwa da mutane 29 a 2009 suka ƙaru zuwa 33 kana a bana an sami mafi yawa 51.

Wannan lamari dai ya shafi duk nahiyoyin ne, musamman ma a nahiyar Afirka, kuma Jean-Francois Julliard ya yi bayanin cewa tun bayan yaƙin Iraƙi farashin neman fansar waɗanda aka yi garkuwa da su ya tashi kana kuma aka sami ƙaruwar cafke 'yan jaridan bisa dalilan siyasa.

Ƙaruwar da aka samu ta hanyar amfani da yanar gizo ya ƙara wa 'yan jarida damar yin amfanin 'yancin albarkacin bakin su, wanda kuma ya kai ga cafke marubuta a dandalin blog 152 a shekarar 2010 wasu 52 kuma suka fuskanci azabtarwa kana ƙasashe 62 suka taƙaita 'yancin amfani da yanar gizo a ƙasashen su.

Julliard ya ce mafi yawancin 'yan jaridan dake kurkuku sun fito daga ƙasashen Afirka ne da sauran ƙasashen da kafofin yaɗa labaran su basu da 'yancin fada a ji, kuma karɓuwan da yanar gizon ya samu a irin waɗannan wuraren ne ya rage yawan mutuwar 'yan jaridun da ke zuwa wuraren ɗaukar labaran gaba da gaba.

A yanzu haka dai Iran ne kan gaba a wurin take 'yancin fadin albarkacin baki, inda 'yan jarida 30 suka yi gudun hijira, sai Eritriya da 'yan jarida 15 wadda kuma ke biye da Somaliya da 'yan jarida 14.

Mawallafi: Pinado Abdu

Edita: Yahouza Sadissou Madobi