Rahoton Human Rights Watch kan rikicin Baga | Labarai | DW | 01.05.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rahoton Human Rights Watch kan rikicin Baga

Hukumar kare hakkin dan adam ta Human Rights Watch ta ce ya kamata a yi cikakken bincike kan tashin hankalin garin Baga a Najeriya da ya yi sanadiyyar rasuwar mutane da dama.

Human Rights Watch Logo

Human Rights Watch Logo

Hukumar ta yi wannan kiran ne bayan da ta fidda wasu hotuna na tauraron dan adam wanda ya nuna girman barnar da aka yi a garin na Baga bayan fafutukar da aka yi tsakanin soji da 'yan kungiyar nan ta Boko Haram.

Wannan dai na zuwa ne kwana guda bayan fitar wani rahoton da wani kwamiti da gwamnati kasar ta kafa don bicike game da rikicin wanda ke cewar farar hula shida ne kawai su ka hallaka yayin da soji su ka hallaka 'yan kungiyar ta Boko Haram talatin.

To sai dai mazauna yankin da su ka shaida faruwar lamarin da kungiyoyin bada agaji wanda ba na gwamnatin ba gami da kungiyoyin fararen hula sun tsaya kan bakan su cewar fararen hular da su ka hallaka sun haura dari biyu.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Yahouza Sadissou Madobi