Rahoto kan hare-haren ta′addanci a duniya a 2014 | Labarai | DW | 19.06.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rahoto kan hare-haren ta'addanci a duniya a 2014

Mutane dubu 33 suka hallaka a cikin hare-haren ta'addanci dubu goma sha ukku da 463 a cikin kasashe 95 na duniya.

Sakamakon rahoton wani bincike da Amirka ta gudanar kan batun ayyukan ta'addanci a duniya a shekara ta 2014 da kuma aka wallafa ranar Jumma'ar nan ya bayyana cewar mutane dubu 33 ne suka hallaka a cikin hare-haren ta'addanci dubu goma sha ukku da 463 da 'yan ta'addar suka kaddamar a cikin kasashe 95 na duniya.

.Rahoton ya kuma ce mutane dubu 34 da 791 suka jikkata a cikin hare-haren sannan mutane dubu tara da 428 aka yi garkuwa da su :Sannan kashi 60 daga cikin dari na hare-haren ta'addancin an kaddamar da su ne a kasashen Iraki da Pakistan da Afganistan da Indiya da kuma Najeriya.Rahoton ya kuma zargi kasar Iran da ci gaba da tallafa wa kungiyoyin 'yan ta'addar a Yankin Gabas ta Tsakiya.