Rade-radin yunkurin juyin mulki a Niger | Siyasa | DW | 24.06.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Rade-radin yunkurin juyin mulki a Niger

Wani cecekuce ya kunno kai tsakanin yan kasa, musamman yan siyasa kan batun bankado wani shiri na shirya makarkashiyar kifar da gomnatin jamhuriya ta Niger.

A jamhuriyar Niger wani cecekuce ne ya kunno kai tsakanin yan
kasar, musamman yan siyasa dangane da batun bankado wani shiri na
shirya makarkashiyar kifar da gomnatin jamhuriya ta Niger. Wasu jaridun
kasar ne guda biyu wadanda ake ganin na da kusanci da fadar shugaban
kasar ta Niger su ka wallafa wanann labari tare ma da buga wata
takarda mai kunshe da bayanan sirrin makarkashiyar da wasu mutane da
ba a bayyana ko su wanene ba, su ke son shiryawa a nan gaba. Sai dai tuni
wasu yan kasar, musamman na bangaren adawa su ka soma zargin gomnatin da shirya wanann makarkashiya domin karkatar da akalar yan kasar daga lura da matsalolin da mulkin na yanzu ya ke fuskanta.

Ainahi dai wasu jaridu ne guda biyu da su ka hada da jaridar l' Opinion
da kuma ta La Roue de l'histoire wasu jaridu biyu masu zaman kansu a
kasar ta Niger su ka rubuta wanann labari tare ma da wallafa kopi na
wasu takardu masu kunshe da bayanai na hanyoyin da masu manufar
hargitsa milkin za su bi domin cimma gurinsu, dama kudade miliyon 49 da
mutanen su ka tanada domin aiwatar da shirin nasu. Tuni kuma wanann
labari ya soma haifar da mahawara a tsakanin yan siyasa da kafofin yada
labarai na kasar ta Niger. Da ta ke tsokaci kan wannn lamari, jamiyyar
PNDS Tarayya, ta bakin Honnorable Zakari Umaru, ko da ya ke ba ta fito
fili ta zargi wani ba, cewa ta yi akwai kanshin gaskiya cikin labarin
domin kuwa biri ya yi kama a mutun.


Ita kuwa da take ke mayar da martani akan wanann batu jamiyyar MNSD Nasara, madugar yan adawa ta bakin Honourable Mamman Ibrahim, fassara kalaman bangaran masu milkin ta yi da wata almara.

Brigi Rafini , Ministerpräsident Niger 2012

Pirayim Ministan Jamhuriyar Niger Brigi Rafini

Wannan dai ba shine karo na farko ba da milkin Alhaji Mahamadou Issoufou ke fuskantar irin wanann barazana tun bayan hawansa. To amma Honourable Zakari Umaru ya bayyana dalillan da ya ke ganin sune ke haifarwa da masu mulkin irin wanann tarnaki, yana mai cewa:

To amma a cewar Mallam Mamman Ibrahim na jamiyyar MNSD, madugar adawa, masu milkin na neman wargi ne da hankalin al'umma domin kuwa da alamu ruwa ya karewa dan kada.

Wannan rade-radi na yinkurin kifar da gomnatin mai ci a yanzu ya zo ne
a daidai loakcin da tashin harbe harbe ke neman zaman ruwan dare a
birnin Yamai, inda ko a makon da ya gabata sai da jama'a su ka shaida
jin karan wasu harbe-harbe da asubahi kusa da fadar shugaban kasa,
harbe harben da har yanzu a hukumance babu wani bayani akansu.

Mawallafi: Gazali Abdou Tasawa
Edita: Umaru Aliyu