Rabon mukamai a Sudan ta Kudu | Labarai | DW | 07.01.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rabon mukamai a Sudan ta Kudu

An cimma yarjejeniyar kan raba madafun ikon a Sudan ta Kudu da nufin samar da zaman lafiya tsakanin gwamnati da 'yan adawa.

A ranar Alhamis din nan ce dai masu saka idanun suka fadi cewar ma'aikatun kudi da tsaro da shari'a da kuma yada labaru za'a za su kasance a hannun mutanen Shugaba Salva Kiir, yayin da jagoran 'yan adawa kuma tsohon mataimakin shugaban kasar Riek Machar zai cigaba da rike mukaminsa.

Har wa yau, mukaman da suka hada da ministocin man fetur da na cikin gida za su kasance a hannun mutanen Machar sannan tsofaffin fursunonin siyasa wanda ba su da nasaba da bangaren Shugaba Kiir ko kuma Machar za su rike mukamin ministan harkokin kasashen waje, yayin da sauran 'yan adawa da ba sa dauke da makamai za su ja ragamar tafiyar da harkokin majalisar zartarwa.