Ra′ayoyin kan sanarwar mutuwar Shekau | Siyasa | DW | 20.08.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ra'ayoyin kan sanarwar mutuwar Shekau

Gwamnati ba ta ce uffan ba game da sanrawar da JTF ta yi cewa watakila shugaban kungiyar da aka fi sani da Boko Haram ya mutu. Sai dai ra'ayoyin al'uma da Kungiyoyin fararen hula sun sha banban a kan wannan batu..

Zance daya ake yi a Kusan dukkakin wuraren zaman al'umma da kasuwanni a arewacin Najeriya: shi ne na sanarwar da rundunar tabbatar da tsaro da aka fi sani da JTF ta fitar wanda ta ce wata kila jagoran Kungiyar da aka fi sani da Boko Haram ya riga mu gidan gaskiya. Kungiyoyin fararen hula da talakawa sun bayyana ra'ayoyin su kan wannan sanarwa inda yawancinsu suka bayyana shakku kan sahihancin mutuwar Imam Shekau wanda a baya gwamnatin Najeriya da ta Amurka suka sanya makudan kudade ga wanda ya ba da bayanai da suka kai ga kame shi ko kuma hallaka shi.

Nigeria Kampf gegen Boko Haram Islamisten

Sojojin Najeriya sun dade da fara yakar Boko Haram

Akwai kuma wasu sassa na 'yan Najeriya da ke bayyana murna da wannan sanarwa saboda a tunaninsu mutuwar shugaban kungiyar da aka fi sani da Boko Haram ka iya kashe wutar wannan rikici.

Karshen rikici ke nan idan shekau ya mutu?

Su kuma Kungiyoyin fararen hula bayyana takaicinsu suka yi kan wannan sanarwa, wacce suke ganin in ba an yi da gaske ba matsalar da ake neman a warwarewa zata kara dagulewa tare da misalai da abubuwan da suka faru da shugaban kungiyar na farko a shekara ta 2009. Barista Abdullahi Muhammad Inuwa shine shugaban kungiyar kare hakkin bani Adama da muhalli ya shaida wa Deutsche Welle cewa idan wannan mataki ya tabbata gaskiya, zai iya kawo karshen duk wani shiri na yin sulhu da 'yan Najeriya ke fata.

An saba bayyana cewa Shakau ya mutu

Wannan dai ba shi ne karon farko ba da ake samun rahotannin mutuwar shugaban kungiyar inda a baya ma ake ce an hallaka shi a wani yanki na kasar Mali. Lamarin da Kungiyar kullum ke musantawa tare da nuna shugaban a faifayin na bidiyo.

PRESIDENT GOODLUCK JONATHAN SHAKING HANDS WITH A MEMBER OF THE COMMITTEE ON DIALOGUE AND PEACEFUL RESOLUTION OF SECURITY CHALLENGES IN THE NORTH, BARR AISHA WAKILI DURING THEIR INAUGURATION AT THE PRESIDENTIAL VILLA ABUJA ON WEDNESDAY (24/4/13). LEFT IS MRS ESTHER CONDA.

Gwamnatin Najeriya ta yi yunkurin yin afuwa ga 'ya'yan Boko Haram

Amma dai jami'an tsaron sun musanta cewa hoton bidiyon da Kungiyar ta fitar ranar 13 ga wannan watan na Agusta dodorido aka yi wa mutane, inda wani ya kwaikwayi shugaban don dai a ci-gaba da karfafa guiwar magoya bayansa. Tambayar da mutane ke yi ita ce ko kashe Iman Shekau shi ne karshen hare-hare da ake dangantawa da Kungiyar Boko Haram da kuma matsalar tabarbarewar tsaro da yanzu haka ta gurgunta harkokin kasuwanci da na yau da kullum?

Mawallafi: Almin Suleiman Mohammad
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe

Sauti da bidiyo akan labarin