Putin ya gana da al-Sisi na Masar | Labarai | DW | 10.02.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Putin ya gana da al-Sisi na Masar

Shugaba Putin dai ya kasance wani shugaba daga kasar da ba ta Larabawa ba da ke mara ba ga shugaba Abdel Fattah al-Sisi, bayan yunkurin murkushe magoya bayan Mohammed Mursi a watan Yulin 2013.

Shugaba Vladimir Putin na kasar Rasha ya gana da takwaransa na kasar Masar a birni alkhahira a yau Talata adaidai lokacin da mahukuntan na birnin Moscow suka shiga inganta dangantaka da kasashen Larabawa musamman wadanda suke takun saka da mahukuntan birnin Washington.

Shugaba Putin dai ya kasance wani shugaba daga kasar da ba ta Larabawa ba da ke mara ba ga shugaba Abdel Fattah al-Sisi wanda ya sha suka mai zafi kan yadda ya kaddamarwa masu aadawa da shi da ke zanga-zangar goyon bayan Mohammed Mursi a watan Yulin 2013.

Wannan dai na zama ziyara ta farko zuwa birnin Al-Khahira da shugaba Putin ya yi cikin shekaru goma inda ya sauka a jiya Litinin, wacce kuma ta biyo bayan juyin juya hali da ya yi awon gaba da Hosni Mubarak da shugaba Putin ya gana da shi a ziyarar da ya kai a shekarar 2005 lokacin yana kan mulki.

A cewar masharhanta wannan ziyara ta Putin na aika sako ne ga mahukuntan birnin Washington cewa ba zai zama saniyar ware ba a tsakanin kasashen duniya duk da rikicin Ukraine.