Premier Ehud Olmert ya bada shaida adangane da yaki da Hizbollahi | Labarai | DW | 01.02.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Premier Ehud Olmert ya bada shaida adangane da yaki da Hizbollahi

Prime minista Ehud Olmert na kasar Izraela ya fara bada bayanan shaida a gaban wata hukuma ta musamman da gwamnatin kasar ta nada ,domin binciken yakin da dakarun Izraelan suka kaddamar akan yan Hizbollahi din kasar Lebanon a shekarar data gabata.Gwamnatin Izraela da dakarunm sojin kasar dai na fuskantar mummunar suka dangane da yadda wannan fada na wata guda ya gudana.Prime minista Olmert dai na mai zama na karshen shaidu kimanin 70 dasu bayyana a gaban wannan hukuma,wadda zata gabatar da kwarya kwaryar rahotanta a tsakiyan watan Maris mai kamawa.