Praministan Mali ya kai ziyara a kasar Tchadi | Labarai | DW | 04.12.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Praministan Mali ya kai ziyara a kasar Tchadi

Tun bayan da saktarin Majaisar Dinkin Duniya Ban Ki-Moon ya nuna damuwarsa ga matakin soji a arewacin Mali,Tarayyar Afrika ta sake salo na neman izinin aikawa da dakarunta

African Union Chief Nkosazana Dlamini-Zuma (front L) and Mali's President Dioncounda Traore attend a high level international meeting in Bamako, October 19, 2012. Regional leaders joined international organisations in Bamako on Friday trying to narrow their differences over whether al Qaeda-linked Islamists in the north of Mali should be dislodged via military intervention or a more gradual political approach. REUTERS/Adama Diarra (MALI - Tags: POLITICS)

Check Modibo Diarra a kasar Tchadi

Shugaban gwamnatin rikon kwarya na Mali Check Modibo Dirra,ya kai wata ziyara a kasar Tchadi inda ya gana da shugaban kasar Idriss Deby Itno da kuma shugaban Tarayyar Afrika bugu da kari shugaban jamhuriyar Benin Thomas Bony Yayi a wani matakin neman kwarin gwiwa ga daukacin kasashen Afrika da su nuna bukatar samun izini daga Majalissar Dinkin Duniya domin aikawa da dakarun kasa da kasa a arewacin Mali inda 'yan kishin islama suka mamaye watani 9 da suka gabata.
Bony Yayi ya kira Majalisar Dinkin Duniya da ta gaugauta ceto al'ummar arewacin Malin daga mawuyacin halin da suke ciki sakamakon cin zarafin da kuma azabar da suke gani da sunan musulunci.

Mawallafi: Issoufou Mamane
Edita : Yahouza Sadissou Madobi