Pistorius zai yi shekaru 13 a kurkuku | Labarai | DW | 24.11.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Pistorius zai yi shekaru 13 a kurkuku

Kotun kolin kasar Afirka ta Kudu ta yanke hukuncin tsawaita wa'adin zaman gidan yari ga zakaran tseren nakasassu Oscar Pistorius, daga shekaru shida zuwa shekaru goma 13 bisa zargin kashe budurwarsa.

Da farko dai masu gabatar da karar kasar Afirka ta Kudu sun kalubalanci hukuncin shekaru shida da Kotu ta yankewa dan tseren da cewa ya yi sassauci,.

Tun da fari dai an yanke wa Pistorius hukuncin shekaru biyar ne bayan kotu ta sameshi da laifin kisa ba da gangan ba a kan buduwar tasa Reeva Steenkamp a shekarar 2013.

Zakaran dan wasan tseren Oscar Pistorius bai halarci zaman kotun na ranar Jumma'a ba, amma kotun ta yanke hukuncin tsawaita shekarun zaman sa a gidan yari tare da zabtare shekarun da ya yi na zaman wakafi a baya.