Pistorius zai shafe shekaru biyar a gidan yari | Siyasa | DW | 21.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Pistorius zai shafe shekaru biyar a gidan yari

Wata kotun kasar Afirka ta Kudu ta yanke wa dan tseren nakasassun nan Oscar Pistorius hukuncin daurin shekaru biyar a gidan kaso bisa samunsa da laifin kashe budurwarsa Reeva Steenkamp bisa kuskure.

Mai shari'a Thokozile Masipa ce ta karanto hukuncin da ta danganta da wanda ya ke ciki da adalci ga Pistorius bayan da aka sameshi da laifin kisa bisa kuskure. Wannan kuma hukuncin shi ne dauri a gidan kaso inda mafi yawan shekarun da zai yi shi ne biyar, bisa la'akari da tanadin dokar miyagun laifuka na 51 na shekara ta 1977 a Afirka ta Kudu.

Hukuncin na biyun da aka yanke wanda ya shafi amfani da makami ba bisa ka'ida ba, ya shafi wani harbi da ya yi ne ba gaira ba dalili a wani wurin cin abinci kafin ma rasuwar budurwarsa Reeva Steenkamp. Yanzu dai bisa wannan hukuncin da aka yanke, Pistorius zai iya fitowa daga gidan kason bayan watanni 10 idan ya yi ladabi.

Oscar Pistorius Urteil Archivbild Reeva Steenkamp und Oscar Pistorius

Soyeyyar Pistorius da Steenkamp ta zama tarihi

Kawun Pistorius Arnold Pistorius ya fadawa masu kawo labarai cewa sun amince da wannan hukunci. Amma kuma ya zargi masu shigar da kara da kokarin raunanasu fiye da irin halin dimuwar da suke ciki, inda suka ce ya kashe budurwar tasa ne da gangan. Sannan ya kara da cewa dukkansu na cikin wani hali na juyayi har yanzu.

Masu shigar da karar dai sun nemi a daure Pistorius na tsawon shekaru 10 ne a gidan kaso.Su kuma masu kareshi sun nemi da a yi mishi daurin talala, ma'ana a samar mishi aiki irin na raya al'umma.

Mai shari'ar dai ta ce wasu daga cikin abubuwan da suka yi tasiri wajen yanke wannan hukunci sun hada da cewa wannan ne karon farko da Pistorius ke laifi. Sannan kuma ya nuna damuwa sosai. Yunkurin da ya yi na ceto budurwarsa bayan da ya ga abin da ya yi, duk abubuwa ne da suka nuna cewa bai so mutuwarta ba.

Sauti da bidiyo akan labarin