Pilipin ta yaba wa Amirka kan ′yan ta′adda | Labarai | DW | 28.02.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Pilipin ta yaba wa Amirka kan 'yan ta'adda

Sashin tsaro na Amirka ya bayyana kungiyoyin Maute da Dawlatul Islamiyah Waliyatul Masrik cikin jerin kungiyoyi na 'yan ta'adda a duniya.

Philipinen Präsident Rodrigo Duterte (Picture-Alliance/AP Photo/Bullit Marquez)

Shugaban kasar Pilipin Rodrigo Duterte dai na fama da masu tada kayar baya

Kasar Pilipin a wannan rana ta Laraba ta yaba da matakin da mahukuntan birnin Washington na Amirka suka dauka wajen ayyana kungiyoyi masu ikirarin Jihadi biyu cikin jerin sunayen ‘yan ta'adda, cikinsu kuwa har da wacce ta mamaye yankin kudancin birnin Marawi a karshen shekara bara. Mayakan da aka dauki lokaci ana ba ta kashi da su tsawon watanni biyu.

Sashin tsaro na Amirka ya bayyana kungiyoyin na Maute da Dawlatul Islamiyah Waliyatul Masrik cikin jerin kungiyoyi na 'yan ta'adda a duniya.

A ranar Talata ce dai Amirkar ta bayyana cewa za ta hana wadanda ke taimaka wa ‘yan ta'addar taba kadadrorinsu a Amirka da ma hana Amirkawa hulda da su.