Pilipin ta kai wa ′yan Abu Sayyaf hari | Labarai | DW | 16.12.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Pilipin ta kai wa 'yan Abu Sayyaf hari

Sojoji 350 na Pilipin sun kaddamar da hari a maboyar mayakan kungiyar masu tsananin kishin addini ta Abu Sayyaf da ke a rukukin dajin tsibirin Basilan mai tazarar kilomita 885 da babban birnin kasar na Manilla.

Hukumomin sojin kasar Pilipin sun bada sanarwar tura da sojoji 350 domin kai hari ga mayakan kungiyar masu tsananin kishin addini ta Abu Sayyaf a maboyarsu da ke a rukukin dajin tsibirin Basilan mai tazarar kilomita 885 da babban birnin kasar na Manilla.

Kakakin sojin kasar ta Pilipin Filemon Tan, ya ce sojin gwamnatin kasar uku sun halaka a lokacin arangama da mayakan Kungiyar ta Abu Saffaf .

Ya kuma kara da cewa ta kaisu ga yin amfani da makaman atilare da jirage masu dirar angulu da motoci masu surke a cikin fadan.

Wasu shaidun ganin da ido sun tabbatar da mutuwar mayakan Kungiyar ta Abu Sayyaf 15 a cikin fadan.