Philippine: Fursinoni da dama sun tsere | Labarai | DW | 04.01.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Philippine: Fursinoni da dama sun tsere

Akalla fursunoni 158 suka fice daga gidan yarin garin Kidapawan da ke a kudancin kasar a lokacin wani hari da membobin wata kungiyar masu kaifin kishin addinin Islama suka kai. 


Gidan yarin da lamarin ya faru dai yana kudancin kasar, kuma a cewar hukumomi fursunonin sun tsere ne a lokacin wani hari da wasu mutane da ake kyautata zaton mambobin wata kungiyar masu kaifin kishin addinin Islama ce suka kai da misalin karfe daya na dare a kasar. 

Mahukuntan kasar wadanda suka tabbatar da afkuwar lamarin sun ce maharan su kimanin 100 dauke da man'yan bindigogi, sun kwashe kimanin sa'o'i biyu suna dauki ba dadi da jami'an tsaron gidan kason birnin na Kidapawan wanda ke a nisan kilomita kimanin 50 Yamma ga birnin Davoa, birni mafi girma na tsibirin Mindanao na kasar ta Phillipine. 

Ana kyautata zaton dai maharan mambobin wata kungiya ce da ta balle daga babbar kungiyar masu kaifin kishin Islama ta Front Moro Islamique de Liberation wato Milf a takaice, wacce ta cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da gwamnatin kasar. Kazalika maharan sun kaddamar da harin ne da nufin kwanto sauran abokanensu da ke tsare inda suka kashe wani jami'in tsaro guda.