Pentagon: Amirka ta hallaka ′Yan al-Shabab sama da dari | Labarai | DW | 07.03.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Pentagon: Amirka ta hallaka 'Yan al-Shabab sama da dari

Ma'aikatar harkokin tsaron Pentagon ta Amirka ta bayyana cewar wani jirgin yakin ta mai sarrafa kan sa da kan sa ya kai wani hari a sansanin horaswa na kungiyar al-Shabab a Somaliya

Kazalika sanarwar ta ce a sakamakon harin sama da mayakan 150 da ke kokarin kai hare-hare a wannan makon da muke ciki aka kashe.

Pentagon din ta ce an kai harin ne a ranar asabar din nan a sansanin da yake nesa da birnin Mogadishu wanda kuma ke da tazarar kilomita 195.

Mai magana da yawun Pentagon Capt,Jeff Davis ya ce mayakan na wani atisaye ne kuma hakan wata babbar barazana ce ga Dakarun hadaka na Amirka da Afrika a yankin.

Kazalika sanarwar ta kara da cewar wata kididiga da aka gudanar tayi nuni da cewar fiye da mayakan al-Shabaab sama da dari 150 ne aka hallaka a 'yan kwanakin da suka gabata.