PEGIDA ta shirya gangami a birnin Vienna | Labarai | DW | 08.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

PEGIDA ta shirya gangami a birnin Vienna

kimanin mutane 250 za su halarci wannan gangami da aka shirya a tsakiyar birnin Vienna na Ostareliya kamar yadda masu shirya zanga-zangar suka fadawa 'yan sanda.

Wani reshe na Kungiyar Pegida mai adawa da yawaitar Musulmi a tsakanin kasashen Turai a Ostiriya, ya bayyana cewa zai gudanar da zanga-zanga a farkon watan Fabrairu mai kamawa, kamar yadda 'yan sanda suka tabbatar a ranar Alhamis dinnan.

Reshen Kungiyar ta Pegida ya fada wa 'yan sanda cewa yana saran kimanin mutane 250 zasu halarci wannan gangami nasu da suka shirya a tsakiyar birnin Vienna a ranar biyu ga watan Fabrairu.

A cewar mambobin wannan kungiya suna gayyatar kowa da kowa, koma daga wace kungiya yake ko ma'aikata ko kasa muddin yana adawa da masu kaifin kishin addinin Islama da shari'ar addinin.

Wannan jawabi dai na fita ne daga shafin Facebook na wannan kungiya.

Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Muhammad Auwal Balarabe