PDP ta lashe zaben jihar Ekiti | Labarai | DW | 22.06.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

PDP ta lashe zaben jihar Ekiti

Jam'iyyar PDP dake mulki a Tarayyar Najeriya ta samu nasarar lashe zaben gwamnan da aka gudanar a jihar Ekiti da ke yankin Kudu maso Yammacin kasar.

Wahlen Nigeria Attahiru Jega

Bayan kammala kirga kuri'un da aka kada a zaben gwamnan da aka gudanar a jihar ta Ekiti dake kudancin Tarayyar Najeriya, rahotanni sun bayyana cewa dan takarar jam'iyyar PDP ne ya samu nasarar lashe zaben da kuri'u mafiya rinjaye.

Da ya ke bayyana sakamakon zaben baturen zabe a jihar ta Ekiti Farfesa Isaac Ozomo ya sanar da cewa dan takarar gwamnan a jam'iyyar PDP Ayodele Peter Fayose ya lashe zaben da kuri'u sama da dubu 200 yayin da abokin hamayyarsa na Jam'iyyar adawa dake zama gwamanan jihar mai barin gado John Kayode Fayemi ya zo na biyu bayan da ya samu sama da kuri'u dubu 120.

Wakilinmu na Lagos Mansur Bala Bello ya ruwaito cewa an jibge jami'an tsaro masu tarin yawa a jihar ta Ekiti gabani da kuma yayin kada kuri'un.

Mawallafi: Mansur Bala Bello
Edita: Lateefa Mustapha Ja'afar