Paul Kagame ya samu sabon wa'adi na uku
August 5, 2017An bada sakamakon na farko ne dai bayan da aka kidaya kashi 80 cikin 100 na kuri'un da aka kada. Abokan takarar na Kagame guda biyu kowa ya samu kasa da kashi daya cikin 100. Sakamakon na farko dai ya nunar cewa mai bi wa Shugaba Kagame wato Philippe Mpayimana ya samu kashi 0.72 yayin da shi kuma Frank Habineza ya samu kashi 0.45 na yawan kuri'un da aka kidaya. Paul Kagame ya kasance mataimakin shugaban kasa sannan ministan tsaron kasar ta Ruwanda kafin majalisar dokokin kasar ta zabe shi a matsayin shugaban kasa a shekara ta 2000 sai kuma a shekara ta 2003 da kuma 2010 ya sake cin zaben inda nan ma ya samu fiye da kashi 90 na kuri'un da aka kada. A yanzu kuma Kagame ya samu wani sabon wa'adin mulki na uku inda zai shafe wasu shekaru bakwai ya na mulkin kasar ta Ruwanda.