Patrice Talon ya lashe zaben shugaban kasar Benin | Siyasa | DW | 21.03.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Patrice Talon ya lashe zaben shugaban kasar Benin

Hamshakin dan kasuwa Patrice Talon ya lashe zaben shugaban kasar Benin da ya gudana zagaye na biyu da kashi 65.39 cikin 100.

Benin Kandidat Patrice Talon vor der Stichwahl für den 16.März

Sabon shugaban kasar Benin Patrice Talon

Sabon shugaban kasar ta Benin Patrice Talon dan shekaru 57 da haihuwa, dan asalin birnin Ouidah na da aure da 'ya'ya biyu, inda bayan karatunsa a fannin ilimin kimiyya a jami'ar birnin Dakar na kasar Senegal. Sai dai bai samu ci gaba da karatun da ya soma a makarantar horas da matukan jirgin sama na farar hula ta ENAC a birnin Paris na kasar Faransa ba, abun da ya dakatar da shi daga burin da yake na zama matukin jirgin sama, inda sabanin haka ya shiga cikin harkokin kasuwanci na takin zamani na noma.

Benin Präsidentschaftskandidat Patrice Talon

Patrice Talon a lokacin yakin neman zabe

Talon ya samu goyon bayan 'yan takara 23 cikin su har da Sébastien Ajavon dan takaran da ya zo na uku a zagaye na farko na zaben. Masu lura da al'ammuran kasar ta Benin na ganin cewa kasancewarsa wanda ya fito daga kabilar Fon da ke a matsayin kabilar tsofon shugaban kasar Nicéphore Soglo, ya taimaka wajan samun wannan nasara ta Patrice Talon. Kuma a baya ya kasance daya daga cikin wadanda suka taka rawa wajan ganin an zabi shugaban kasar mai barin gado Thomas Boni Yayi inda ya tallafa masa da kudaden yakin neman zabe a shekara ta 2006 da kuma 2011.

Tuni dai Firaministan kasar mai barin gado kuma dan takara a zagaye na biyu na zaben shugaban kasar Lionel Zinsou wanda ya samu kashi 34.61 cikin 100 ya amsa kayen da ya sha a zaben inda ta wayar tarho ya kira sabon zababben shugaban kasar domin taya shi murna.

Benin Präsidentschaftswahl Kandidat Lionel Zinsou

Firaminista Lionel Zinsou kuma dan takara a zagaye na biyu na zaben

"Na kira Patrice Talon da yammacin wannan rana domin taya shi murna kuma na tabbatar mishi cewa, kuma na sanar da shi cewa a shirye nake mu fara shirye-shiryen mika mulki."

Tuni dai aka fara samun martani daga kasashen waje, inda Shugaban kasar Faransa Francoise Hollande ya jinjina wa yadda demokaradiyyar kasar ta Benin ke tafiya ganin yadda aka gudanar da zaben cikin tsanaki. Shugaban Hollande ya yi fatan alheri zuwa ga sabon zababben shugaban kasar ta Benin Partice Talon inda yake fatan ganin kyaukyawar huldar da ke tsakanin kasashen biyu ta dore musamman ma a fannin makamashi, tafiyar da kyaukyawan mulki, da kuma yaki da ta'addanci. Kotun tsarin mulkin kasar ta Benin ce dai za ta tabbatar da wannan sakamako nan da 'yan kwanaki masu zuwa.

Sauti da bidiyo akan labarin