Park Geun Hye ta sami nasara a zaɓen Koriya ta Kudu
December 19, 2012Talla
A cikin kishi sama da tamanin na ƙuri'un da aka ƙidaya ta samu kishi 51 da yan ka a gaban abokin hamayarta Moon Jae In wanda tuni ya amince ya sha kaye
Park yar tsohon shugaban gwamnatin mulkin kama karya Park Chunk Hee wanda ya zo akan karagar mulki a shekara ta 1961 kafin a kashe shi a shekara ta 1979.Zata kasance mace ta farko da za ta riƙe matsayin shugaban ƙasar da za ta fara wa'adin mulki na shekaru biyar a cikin watan feberu na tafe.
sama da mutane miliyion 40 ne dai suka kaɗa ƙuri'u a zaɓen shugaban kasar da aka ce jamaa da dama sun fito.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Usman Shehu Usman