1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Limamin cocin Katolika ya gana da jagoran Shi'a a Iraqi

March 6, 2021

Jagoran mabiya mazahabar Shi'a a Iraqi Ayatollah Ali al-Sistani ya yi kira ga hukumomi su kare 'yancin Kiristoci a kasar bayan ganawarsa da babban limamin cocin Katolika Paparoma Francis a wannan Asabar.

https://p.dw.com/p/3qIVw
Irak Najaf | Besuch Papst Franziskus | Treffen mit Großajatollah Ali al-Sistani
Hoto: Grand Ayatollah Ali al-Sistani office/Reuters

A yayin ziyarar da Paparoma Francis din ya kai wa al-Sistani  a garin Najaf da ke Iraqin, al-Sistani  ya ce ya kamata Kiristoci su yi rayuwarsu kamar yadda kowane dan Iraqi yake da 'yancin yin walwala a kasar.


Paparoma Francis din ya gode wa jagoran Shi'an na Iraqi, a kokarin da yake yi na ganin an kare rayukan tsiraru da ake gallaza wa a cikin al'umma.


A baya dai akwai kimanin Kiristoci kusan miliyan daya a Iraqi, amma tun bayan kutsawar da Amirka ta yi a kasar a shekara ta 2003 da kuma rikice-rikicen addinin da suka biyo bayan hakan, sai yawan Kiristocin yanzu ya koma tsakanin 250,000 zuwa 400,000.


Limamin cocin Katolikan dai na ziyarar kwanaki hudu ne a Iraqi a wani mataki na samar da zaman lafiya da fahimtar juna a tsakanin Kiristoci da Musulman kasar.