Paparoma ya ji takaicin yawan kisan Krista a duniya | Labarai | DW | 05.04.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Paparoma ya ji takaicin yawan kisan Krista a duniya

Paparoma Francis, ya yi amfani da lokacin Paska wato Ista wajen yin tur da kisan Kristoci a duniya

Shugaban mabiya darikar Katolika na duniya Paparoma Francis, ya yi amafani da lokacin addu'o'in Paska wato Ista na bana, wajen yin tur da kisan Kristoci a duniya ba tare da wata hujja ba.

Haka nan ma Paparoman ya yi Allah wadai da rashin kulawa da kasashen duniya suka nuna ga kisar daliban jami'a 148 galibinsu Kiristoci da mayakan Al Sahbbab suka yi a gabashin kasar Kenya, a Alhamis din nan da ta gabata.

Paparoman ya kuma bayyana rashin jindadi ga hare-hare kan Kristoci a kasashe irinsu Iraki da Libiya da Pakistan dama Najeriya, inda ya ce ba a jin kasashen musulmi da gwamnatocin kasashen yamma na sukar lamarin, sam.

Jagoran Kristan na Katolika, haka nan ya yi amfani da lokacin na Ista, wajen yin kiran kawo karshen fitintinun duniya na tashin tashin tashina a kasashen Larabawa da Ukraine da Najeriya dama kasar Sudan ta Kudu .