Paparoma ya fara ziyarar wasu kasashen Asiya | Labarai | DW | 13.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Paparoma ya fara ziyarar wasu kasashen Asiya

Paparoma yana ziyara a kasashen Siri Lanka da Pilipin

Shugaban Kiristoci mabiya darikar Katolika Paparoma Francis ya nemi kara himma kan kare hakkin dan Adam, yayin da ya fara ziyarar kasashen Asiya da kasar Siri Lanka, inda ya nemi gafarta wa juna a kasar da take murmurewa daga yakin basasa.

Wannan ziyarar tana zuwa lokacin da sabon shugaban kasar Maithripala Sirisena ya lashe zaben makon jiya, kuma Paparoman ya samu gagarumar tarba daga makada, da 'yan makaranta da mabiya addinai daban-daban gami da sauran al'umar kasar ta Siri Lanka. Daga nan Paparoma Francis zai kai ziyara zuwa kasar Pilipin.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Mohammad Nasiru Awal