Paparoma ya bayyana inda ya sa a gaba | Labarai | DW | 16.03.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Paparoma ya bayyana inda ya sa a gaba

Paparoma Francis ya gana da jami'an kafofin watsa labarai a fadar Vatican inda ya bayyana fatan ganin cocin Romankatolika ya zama muryar talakawa a duniya karkashin mulkinsa.

Paparoma Francis ya yi fatan ganin karkashin shugabancinsa cocin katolika ya kaskantar da kansa domin yi wa talaka aiki tukuru. Shugaba na 266 na darikar Romankatolika ya yi wannan furucin ne lokacin da ya gana da wakilan kafofin da ke farautar labarai a fadar Vatican. Paparoman wanda tsohon cardinal na birnin Buenos aires na kasar Argentina ne, ya fayyace wa 'yan jarida dalilan da suka sa shi zaban sunan mulki na Francis, inda ya ce wani talaka ne da ke da ra'ayin tabbatar da zaman lafiya a duniya.

Tun dai bayan da aka zabe shi a matsayin paparoma, Francis ya ke nuna alamun kawo sauyi a harkokin tafiyar da darikar Romankatolika. A mako mai zuwa ne paparoma zai ziyarci wanda ya gabace shi a wannan mukamin wato tsohon paparoma Benedikt na 16 mai murabus. Da ma dai ya buga masa waya tun ranar da aka zabe shi a matsayin paparoma domin sada zumunci tsakaninsu. Paparoma Francis zai gana a ranar Liitinin mai zuwa da shugabar kasarsa ta asali wato Cristina Kirchner ta Argentina.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Halima Balaraba Abbas