Paparoma Francis zai sha rantsuwar kama aiki. | Labarai | DW | 19.03.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Paparoma Francis zai sha rantsuwar kama aiki.

Dubun dubatar jama'a ne za su halarci adu'o'in da bikin rantsar da sabon Paparoma, tare da halartar wasu shugabannin ƙasashen duniya.

Pope Francis approaches priests with an Argentine flag as he arrives in Saint Peter's Square for his inaugural mass at the Vatican, March 19, 2013. Pope Francis celebrates his inaugural mass on Tuesday among political and religious leaders from around the world and amid a wave of hope for a renewal of the scandal-plagued Roman Catholic Church. REUTERS/Stefano Rellandini (VATICAN - Tags: RELIGION POLITICS)

Paparoma Francis, ke kan hanyar zuwa wajen rantsuwar kama aiki

Yau aka shirya za a ƙaddamar da bikin rantsar da Paparoma Francis, sabon jagoran yan ɗarikar Roman Katolika, kwanaki shidda bayan zaɓen sa akan matsayin. Ana tsammanin dubun dubatan jama'a za su yi dafifi a dandalin Sainte Peter da ke a birnin Rome, domin hallarta adu'o'in da bikin rantsar da sabon Paparoma.

A cikin waɗanda aka shirya za su hallara sun haɗa da mataimakin shugaban ƙasar Amirka Joe Biden da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da na Faransa da Spain da kuma shugaba Robert Mugabe na Zimbabuwe. Duk kuwa da cewar ya na a ƙarkashin wani takunkumi na haramta yin zirga-zirga zuwa nahiyar Turai tun a shekarun 2002. An baza 'yan sanda da sojoji har kusan dubu uku a dandalin na Saint Peter domin kula da tsaro.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Usman Shehu Usman